<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Muna roƙon Ubangiji Allah
 Domin salamar Yahudawa yau.

[V2]
 2) Al'umma ce wadda ka zaƃa fa
 Domin su zama mutanenka dai.

[V3]
 3) Amma sun ƙi su karƃe ka a dā.
 Sun juya maka baya, sun ƙi ka.

[V4]
 4) Ka hore su, ka warwatsad da su
 A fuskar duniya duka ko'ina.

[V5]
 5) Yanzu kuma ga lokaci ya yi
 Da za su koma Urushalima.

[V6]
 6) Yanzu ga su a cikin zafin rai
 Har lalle ba su san abin yi ba.

[V7]
 7) Mun sani fa kai kana ƙaunarsu,
 Ka taimake su, mutanenka yau.</lyrics>
<title>Muna Roƙon Ubangiji Allah LW342</title>
<hymn_number>342</hymn_number>
</song>